Likitoci a Isra’ila sun yi wa Firaminsta Benjamin Nethanyahu allurar rigakafin cutar Korona. Hakan na dada bude kofar soma yi wa ‘yan kasar allurar rigakafin cutar.
‘Yan lokuta da yi wa Firaministan kasar allurar, ya shaidawa manema labarai matakin da hukumomin Isra’ila suka dau na karfafa matakan kulawa musamman bangaren kiwon lafiya a filin tashi dama saukar jiragen sama da kuma gudanar da gwaji ga duk wani matafi daga ciki dama wajen kasar ga baki daya.