Firaministan Lebanon Sa’ad Hariri ya ce zai yi murabus daga mukaminsa sakamakon zanga-zangar da aka kwashe makonni biyu ana yi a fadin kasar.
Zanga-zangar da ake yi a fadin Lebanon ta biyo bayan yunkunrin gwamnatin wanda ta janye na sanya haraji a kan kiran waya ta manhajar WhatsApp.
Kasar Lebanon na daga cikin kasashe da bashi ya fi yi musu katutu a duniya.
Zanga-zangar ta yi sanadiyyar rufe bankuna na kwanaki 10, baya ga wasu ofisoshi da makarantu da aka rufe sakamakon hakan.