By Abbas Yakubu Yaura
Firaministan rikon kwarya na Libya Abdul Hamid Dbeibah a ranar Lahadi ya gabatar da bukatarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a wata mai zuwa duk da hana shi gudanar da zabe karkashin dokokin da ake dasu a yanzu.
Ana son Abdul Hamid Dbeibah ya jagoranci kasar har sai an bayyana wanda ya yi nasara bayan zaben shugaban kasa a ranar 24 ga watan Disamba.
Shi ne dan takara na baya-bayan nan daya fito a zaben. Ya gabatar da bukatarsa kwana daya kafin ranar 22 ga watan Nuwamba.
A yau na gabatar da takardar tsayawa takara, domin in yi muku hidima ba don komai ba, domin zaben shugaban kasa mai zuwa, kuma muna rokon Allah Ya taimake mu baki daya don amfanin kasa da al’ummar wannan kasa mai girma.” a cewar Hamid Dbeibah.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An hana dan kasuwa mai karfin fada a ji daga yammacin birnin Misrata tsayawa takara a karkashin dokokin zaben kasar Libya a halin yanzu.sai dai Hamid Dbeibah dai ya yi alkawarin cewa ba zai nemi mukami a zaben ba a matsayin sharadin karbar mukaminsa na riko a farkon wannan shekarar.
Domin samun cancantar ya kamata ya dakatar da kansa daga aikin gwamnati akalla watanni uku kafin ranar zabe, wanda ya kasa yin hakan.sai dai Dbeibah ya shaida wa manema labarai cewa yana jin alhakin ci gaba da sake gina kasar, wanda yakin basasa na tsawon shekaru ya wargaza.
Sai dai kuma Babu tabbas ko hukumar zaben kasar za ta amince da takararsa.
A farkon wannan watan, ‘yan takara da dama ne suka taru, ciki har da Seif al-Islam, dan magajin Gadhafi.
Kwamandan soji Khalifa Hifter, wanda ya yiwa babban birnin Tripoli kawanya kusan shekara guda a shekarar 2019 shi ma yana cikin jerin sunayen wadanda suka tsaya takara.
Kazalika An nada Dbeibah ne a yayin tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a watan Afrilu domin ya jagoranci bangaren zartarwa na gwamnatin rikon kwarya wanda kuma ya hada da majalisar shugaban kasa mai mutane uku karkashin jagorancin Mohammad Younes Menfi, jami’in diflomasiyyar Libya daga gabashin kasar.