By Abbas Yakubu Yaura
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok wanda hokumomin soji suka saki ya fada a ranar Litinin cewa zai samu ikon kafa gwamnati mai cin gashin kanta.
Kalaman nasa sun faru ne kwana guda bayan ya kulla yarjejeniya da sojojin da kusan wata guda suka yi juyin mulki tare da tsare shi a gidan yari.
Hamdok, wanda aka sake zaba a matsayin firaminista tare da majalisar koli ta kasar Sudan, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta siyasa a ranar Lahadin data gabata, domin kawo karshen rikicin gudanar da aikin daya biyo bayan tsoma bakin sojoji a ranar 25 ga watan Oktoba.
A wani bangare na yarjejeniyar, Burhan ya soke matakin daya dauka na korar Hamduk a matsayin Firaminista.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ofishin Firaminista Hamduk yace ya fara gudanar da aikinsa a hukumance.
“Wannan wani muhimmin bangare ne na yarjejeniyar siyasa da muka rattaba hannu, cewa Firaminista ya kasance yana da ikon kafa gwamnati mai cin gashin kanta ba tare da wani matsin lamba ba. Wannan shi ne abin da muka sanya hannu a kan yarjejeniyar.”
Ina so in yi magana a zahiri, ba ni da wani buri na kaina, na ci gaba da zama shugaba ko shiga wata jam’iyya ko ƙungiya, ko kuma in sami farin jini sosai. Alhakin da aka dora min a kafadu ne kawai ke tafiyar da ni. Buri da fatan al’ummar Sudan ne kawai ke jagoranta,” in ji Abdalla Hamdok, Firaministan Sudan da aka maido da shi kan mukaminsa.
A cewar majiyoyin likitocin Sudan, tun bayan juyin mulkin watan Oktoba, akalla mutane 41 ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar.
“Yarjejeniyar wani bangare ne na magance matsalar domin wannan yana bukatar mafita, jawabin Hamdok yana da gamsarwa saboda ya ga yadda ake kashe matasa a tituna kuma kasar nan na komawa baya, wanda hakan ba zai haifar da gyara ba.” Inji Omar Sayed. dan kasar Sudan.Wasu irin su Ahmed Seif dan kasar Sudan sun bayyana rashin jin dadinsu.