Yanzu haka dai ana zaman dar-dat a Sabongari, dake jihar Kano inda wani abu ya fashe da sanyin safiya.
Dimokuradiyya ta ruwaito yadda fashewar ta afku a gefen wata makarantar firamare ta haifar da tashin hankali a cikin al’umma.
A yayin da wasu rahotanni ke cewa an kai hari a wata makaranta, iyayen sun garzaya zuwa makarantun yankin domin kwashe ‘ya’yansu.
An kuma rufe shagunan, inda wasu rahotanni ke cewa tuni matagari ke cin gajiyar hayaniyar suna kutsawa cikin gidajen mutane da shaguna.
Akwai bidiyon daliban da ke yawo a kan tituna sanye da kayan sawa da jini suna yawo a kafafen sada zumunta.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ce ya isa wurin, inda ya cimma an kwashe daliban makarantar Winners School da ke Kano.
Fashewar ta faru ne a kusa da makarantar.
A wani labarin na daban.
Buhari ya yiwa Ƙasar nan duk abinda ya kamata — Wani Ɗan Majalisa a Katsina
Ɗan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Funtua/Ɗandume a Jahar Katsina Muntari Dandutse yace Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi aiki mai kyau a matsayin sa na Shugaba.
Ya bayyana cewa wannan dalilin ne ya sanya Jam’iyyar APC keda ƙarfi a Katsina, duk da Canja Sheƙa da ɗaya daga cikin Sanatocin Jahar.
Dandutse yayi magana akan Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Katsina ta Arewa inda Buhari ya fito, Sanata Ahmed Kaita wanda a watan Afrilu ya sanar da canja sheƙar sa daga Jam’iyyar APC Mai Mulki zuwa Jam’iyyar PDP.
Dandutse yayi zargin cewa Babba Kaita da sauran su da ke Son kawo tangarɗa, suna yi ne domin cimma muradun su, kuma ƴan siyasa ne da basa bin Dokoki da sharuɗɗa.
Ɗan Majalisar ya bayyana haka a Abuja, bayan ya miƙa Fom ɗin sa na Takara domin neman Takarar APC a Kujerar Sanata a Babban zabe na Shekarar 2023.
Ɗan Majalisar yace domin ƴan Najeriya su ciyar da Ƙasar su a gaba, suna buƙatar jefar da bambance-bambancen kabilanci da Addini.