Shahrarren mai shirya wasan Sinima na kasar Faransa Jean-Paul Belmondo ya rasu a wannan Litinin a gidansa da ke birnin Paris yana da shekaru 88 a duniya.
Belmondo, wanda aka haifa a 1933, daya ne daga cikin shahrarrun masu fitowa a fina-finai a farkon shekarun 1970, kuma kafin rasuwarsa ya shirya fina-finai akalla 80 da aka fassara cikin harsuna daban-daban na duniya.
Wasu daga cikin fina-finansa da suka yi fice sun hada da “A bout de souffle”, “Le Guignolo” da dai sauransu, fina-finan da wasu daga ciki ke kasancewa na nishadi da kuma camama don faranta ran masu kallo, yayin da mafi Faransawa ke kiran sa da suna Bebel ko kuma Le Magnigifique sakamakon yadda yake daukar kasada a cikin fina-finansa.
Lauyan Jean-Paul Belmondo Michel Godest, ya ce Marigayin ya rasu ne bayan share dogon lokaci yana jinya da kuma nuna alamun gajiya.
Alkalumma dai sun tabbatar da cewa a tarihi, an sayar da tikitin shiga Sinima fiye da milyan 130 don kallon fina-finan Belmondo a cikin shekarun da suka gabata.
A 2010, Belomondo ya samu kyautar yabo da ake kira Film Critics Association a birnin Los Angeles na Amurka, kafin ya sake lashe kyautar gasar fina-finai mafi girma a duniya wato Cannes Film Festival a 2011.