Tsohon Shugaban Sashen Kimiyyar Siyasa da Nazarin Kasa da Kasa a Jami’ar Ahmadu Bello ABU dake Zaria, Farfesa A. D. Yahaya ya rasu.
Ya rasu ne a ranar Asabar din data gabata, a wani asibiti da ke Abuja, kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sai dai haryanzu majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, ba a San musabbabin mutuwarsa ba.
Farfesa Yahaya shine tsohon Babban Darakta na Kungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantu ta Nigeriaa ASCON.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta tabbatar da Garkuwa da Mutane 3 a Kogi
Kazalika Ya kuma kasance mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa ga marigayi Muhammadu Abubakar Rimi, Tsohon gwamnan jihar Kano a jamhuriya ta biyu.
Masana a ciki da wajan Nigeria na bayyana mamacin, a matsayin mutum mai ban mamaki, kuma fitaccen masanin a kan fannin siyasa.
A wani labarin Kuma na daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Lahadi, ta sanar da cewa ta samu nasarar cafke wasu mutane 21 da ake zargin shahararun ‘yan fashi da makami ne da kuma abokan hadin gwiwa 48 yayin gudanar da samamen da ta kai a cikin watan Satumba.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda SP Muhammed Shehu, a jihar shine wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Gusau, kan nasarorin hukumomin tsaro a jihar.A cewar sa an kuma kashe ‘yan bindiga biyar a jerin sunayen da jami’an tsaron suke nema.
“Tun bayan aiwatar da sabbin matakan tsaro na Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, wata guda daya gabata ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kai hare hare kan wuraren da aka gano maboyar ‘yan bindiga ne dan kawar da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka daga cikin jihar.sannan an daina biyan diyya ga ‘yan ta’adda ta hanyar dangantakar wadanda aka yi garkuwa dasu saboda yadda ake aiwatar da matakan tsaro, ta yadda sadarwa tsakanin ‘yan fashin da masu yi musu bayani ya zama mai wuya, “in ji Shehu.
Kazalika ya kara da cewa, a sakamakon haka, wadanda aka sace sun zama abin dogaro ga ‘yan bindigar kuma an sake su ba tare da wani sharadi ba, bayan da aka gudanar da bincike da inda ‘yan sanda suka ceto su.
Shehu yace, ‘yan sanda ta hanyar aikin da suke ci gaba da yi, sun yi nasarar cafke shahararrun’ yan bindiga 21 a wurare daban daban na jihar, inda aka kashe biyar daga cikin ‘yan bindigar yayin farmakin, a wurare daban daban, an yi musu bayani kuma sun sake saduwa da danginsu.
A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don tabbatar da matakin da kowanne daga cikin wadanda ake zargin ya shiga hannu daga nan za a gurfanar da su a gaban kuliya daban daban, sannan Shehu ya yi kira ga mazauna yankin da su yi hakuri tare da baiwa hukumomin tsaro goyon bayan da ake bukata don kawar da duk masu laifi a jihar, dan dawowar doka da oda.