By Abbas Yakubu Yaura
Kwamitin Manyan Daraktocin Likitoci da Daraktocin Likitoci na manyan asibitocin gwamnatin tarayya sun yi kira da a fito da wata manufa ta musamman kan sauya ma’aikatan lafiya cikin gaggawa ba tare da jiran izni ba.
A cikin sanarwar bayan taro karo na 96 na yau da kullum da kuma taron shekara-shekara karo na 10 a ranar Asabar a Abuja, kwamitin yace shugabannin manyan jami’an kiwon lafiya na tarayya su aiwatar da manufar.
Kungiyar a cikin sanarwar wacce shugabanta mai barin gado, Dakta Jaf Momoh ya karanta, tace yawan fitan ma’aikatan lafiya daga asibitocin su ya zama abin damuwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwamitin ya kuma ce babu wani kokari daya kamata a yi don shawo kan yuwuwar yaduwar kwayar cutar COVID-19 a kasar, yana mai karawa da cewa asibitocin suna da isassun kayan aiki don sarrafa lamuran.