Saudiyya ta bayar da rahoton karin mutum 1,362 da suka harbu da cutar krona cikin sa’a 24 da suka gabata, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar kasar.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ma’aikatar lafiyar na cewa an samu karin mutum bakwai da suka mutu da kuma 210 da suka warke.
Birnin Madina ne kan gaba a yawan sabbin wadanda suka kamun na ranar Asabar, inda aka samu 249, sai Jeddah da ke biye masa da mutum 244 da kuma Riyadh mai 161.
Jumillar wadanda suka harbu da cutar korona a Saudiyya sun kai 25,459, sai kuma wadanda suka mutu 176. Kazalika 3,765 sun warke.
-BBC HAUSA