Cibiyar dake yaki da cutuka masu yaduwa ta Nijeriya NCDC ta fitar da cewa mutum 1, 588 ne suka sake kamuwa da cutar korona a Nijeriya, inda yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar a Nijeriya suka kai 139,242.
NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Asabar.
NCDC ta ce tun bayan bullar cutar a Nijeriya adadin wadanda ake yiwa gwaji na kara karuwa ne, a yayin da kuma kayayyakin ayyukan gwajin ke kara bunkasa. Wanda suka ce wannan shi ne dalilan da ya sanya ake ganin masu kamuwa da cutar ke karuwa.
NCDC ta ce ya zuwa yanzu an yiwa mutum 1,302,410 gwajin cutar tun bayan bullar cutar a ranar 27 ga watan Fabarairun 2020.
Sai dai a alkaluman ranar Asabar din, an sake samun mutum shida da cutar ta kashe cikin awa 24. Inda adadin wadanda cutar ta kashe a halin yanzu suka kai 1,647 a fadin kasar.