Mukaddashin hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) Marshal Dauda Biu, ya bukaci jami’an hukumar da su tabbatar da cewa ma’aikatan da ke karkashinsu sun kasance ba tare da nuna banbancin siyasa ba, tare da kaucewa duk wani nau’i na shiga gangamin siyasa da yakin neman zabe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hukumar ta kuma gargadi jami’an nata da kauracewa rikiyar ayarin motocin yan siyasa.
A cikin wata sanarwa da jami’in kula da wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa sun yi hakan ne domin su sanya aikin su a daidai lokacin da ayyukan zaben 2023 ke kara ta’azzara a fadin kasar.
KARANTA ANAN: Mun Gab Da Kammala Gidajen Gyaran Hali Mai Cin Mutane 9,000 – FG
Biu ya bayar da wannan umarni ne dangane da dokar hukumar FRSC wacce ta bayyana matsayin hukumar a matsayin hukumar da ba ta da alaka da siyasa.
Ya ce an kafa hukumar ta FRSC ne kawai don samar da muhimman ayyuka ga dukkan ‘yan kasa, ba tare da la’akari da muradunsu na siyasa ko wakilcin su ba.
Ko da yake, rundunar ta umurci jami’anta da kwamandoji da su kula da halin da masu amfani da hanyar ke ciki da kuma shirya yadda za a magance duk wata matsalar cunkoson ababen hawa da ka iya tasowa sakamakon ayyukan siyasa.
Ya kara da cewa ya kamata su tabbatar da tura ma’aikata isassu domin saukaka zirga-zirga ta hanyar kula da zirga-zirgar ababen hawa da kwantar da hankula.
Biu ya tabbatar wa al’umma cewa a shirye suke wajen ganin an tabbatar da tsaro a kowane lokaci tare da gargadin su da su bi ka’idojin zirga-zirgar a kodayaushe.
A wani labarin kuma: Hukumar Premier Ta Dakatar Da Wasan Manchester United, Chelsea
Hukumar gudanarwar Gasar Firimiyar Kasar Ingila ta fitar da wata sanarwar dake bada tabbacin cigaba da buga wasannin mako na 8 a karshen makonnan.
Sai dai uku daga cikin wadannan wasanni an dakatar da buga su.
An dai dage wasannnin ne domin girnama mutuwar Sarauniyar Ingila ta biyu wato Elizabeth.