Akalla Fulani makiyaya dubu 4 suka tsere daga yankin Kudancin Najeriya domin kauce wa munanan hare-haren da ake kai musu saboda zargin aikata laifuffuka a yankin.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya jiyo daga bakin Hussaini Abdullahi, jami’in Hukumar Agajin Gaggawa a Jihar Kaduna na cewa, sun tantance Fulani makiyaya kusan dubu 4 da suka isa Jihar tasu, yayin da wasu ke ci gaba da kwararowa.
Abdullahi ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna za ta taimaka musu wajen ganin ta sake tsugunar da su, inda yake cewa babbar bukatarsu ita ce abinci da matsuguni, saboda yadda suka bar mazauninsu ba tare da komai ba.
Haruna Usman Dugga, shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Jihar ya ce an ajiye makiyayan a dajin gwamnati da ake kira Labduga, kuma sun kai iyalai 150 da yawan su ya kai dubu 4.
Gwamnonin Arewacin Nijeriya sun bukaci gudanar da taro da takwarorinsu na kudu da zummar samo maslahar magance rikicin da aka samu na Fulani makiyayan da kuma zarge-zargen da ake musu na aikata laifuffuka.