By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sanye da kakin ‘yan sanda a ranar Lahadin da ta gabata, sun kai farmaki kauyen Ibite Awhum, da ke karamar hukumar Udi ta Jihar Enugu inda suka yi garkuwa da wasu Alhazan Kiristoci guda shida.
Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa an yi garkuwa da mutanen ne a kusa da wani gidan ibada a garin.
Wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun kwashe alhazan da rana tsaka a lokacin da suke addu’a a wani tsauni mai farin jini da ke kusa da gidan sufi inda suka kai su cikin dajin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalejin Fasaha Ta Jihar Osun Ta Samu Sabon Mukaddashin Shugaba, Odetayo
Sai dai rahotannin da ke fitowa daga al’ummar yankin a ranar Talata sun nuna cewa an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su ne biyo bayan kwazon da jami’an tsaron dajin suka yi a kananan hukumomin Udi da Enugu ta Gabas.
Wani alhaji da lamarin ya faru a gaban idonsa amma ya yi nasarar tserewa ‘yan fashin, an ce ya tayar da hankulan mutanen kauyen.
An ce jami’an tsaron sun dauki matakin ne nan take da suka samu labarin tare da bin sawun masu garkuwa da mutane.
Wata majiya ta ce jami’an tsaron dajin da ke yankin sun bi sawun barayin inda suka tuntubi takwarorinsu na Ogbeke Nike da ke karamar hukumar Enugu ta Gabas, wadanda su ma suka yi gangami daga nasu ban garen zuwa cikin dajin.
Da alama dai ganin an yi musu kaca-kaca daga bangarorin biyu, an ce masu garkuwar sun gudu sun bar wadanda aka kama su kadai a sansaninsu inda masu gadi suka gano su, tare da wani da wanda abin ya faru dashi.
Da suke bayyana irin halin da suke ciki, wadanda abin ya shafa da aka kai su gidan sufi, sun ce suna addu’o’i ne a kan tudu, inda suka kara da cewa kwatsam sai ga wasu Fulani su bakwai sanye da kayan ‘yan sanda.
Sun ce ‘yan fashin sun kwashe dukkan wayoyinsu sun umarce su da su shiga dajin.
Sun ce bayan doguwar tafiya, sai suka shiga sansanin ‘yan fashin a cikin dajin, inda abokan aikinsu kusan goma ke jiran su.
Sun kuma samu wani da aka yi garkuwa da shi a can.
A cewar wadanda abin ya shafa, saboda dalilan da ba su sani ba a lokacin, kwatsam sai da masu garkuwar suka shiga cikin dajin, suka bar su su kadai, suka rude kafin masu gadin dajin su bayyana.
Majiyar ta bayyana cewa an sanar da gwamnatin jihar kan lamarin.
A halin yanzu dai, rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.