Wasu kungiyoyi na Fulani makiyaya sun yi zargin cewa ana cin zarafin su tare da kashe su a garuruwan da suke zama a jihar Ebonyi, kuma gwamnatin jihar ta yi biris kan lamarin ba tare da wani yunkuri na daukar mataki ba.
Wasu daga cikin makiyayan kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito, sun shaidawa BBC a ranar Laraba cewa a shekarar 2020, akalla makiyaya 21 aka kashe tare da kona gidajensu kuma rundunar ƴan sanda da gwamnatin jihar sun kasa daukar mataki ko gurfanar da masu laifin.
“Ba a dade ba, suka dawo suka kashe mana shanu biyu. Biyo bayan wannan, muna ta fuskantar barazanoni na cewar za su dawo su kona gidajen mu, bayan sun yi hakan ga wasu ƴan uwanmu da ke a wasu garuruwan jihar.
KARANTA WANNAN: Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dake Dutse Ta Ayyana Ranar Komawa Makaranta
“Akan wannan dalilin, muna rayuwa cikin fargaba. Duk lokacin da muka fita, iyalan mu na fargabar kawo masu hari. Wannan shi ne dalilin mu na yin wannan hijirar. Muna da yawa, ba zan iya bayar da adadin mutanen da ke yin hijirar ba.
“A jihar Ebonyi a shekarar 2021, makiyaya 21 aka kashe kuma.ba za mu iya ƙiyascin yawan dabbobin mu da aka kashe da hare haren da aka kawo mana ba, kuma babu wanda rundunar ƴan sanda ta dauki mataki akai, duk da cewa a mafi akasarin lokuta, rundunar ce ke gano gawarwakin bayan an kashe su.
“Game da shanu idan an kashe su, yan sanda za su zo su tabbatar da faruwar lamarin har ma su dauki bidiyo,” a cewar wani daga cikin masu yin hijirar.
Wani daga cikin shuwagabannin makiyayan ya bayyana cewa suna samun rahotanni na hare haren da ake kaiwa makiyaya a jihar Ebonyi. Ya ce babu yankin da ba a kai masu hari a jihar in banda yankin Eli inda Fulani da mutanen yankin ke zaune cikin lafiya.
Makiyayan sun musanya duk wani zargi da ake yi masu na aikata ba daidai ba dangane da shiga gonakin mutane ba bisa ƙa’ida ba, suna masu cewa babu makiyayan da ya fi ƙarfin doka, kuma duk wanda aka kama da irin wannan laifi, doka ta hukunta shi.