Fursunoni 228 sun tsere daga gidan yarin gyara halinka da ke Koton-Karfe na jihar Kogi bayan aukuwar ibtila’in ambaliyar ruwa da ya rutsa da su a gidan yarin.
Rahotanni sun ce, ambaliyar ruwan wanda ta auku sakamakon ruwan sama mai karfin gaske, ta lalata wani bangare na katangar gidan yarin, abin da ya bai wa fursunonin damar arcewa.
Tuni aka jibge jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda domin aikin ceto, yayin da kuma aka yi nasarar cafke fursunoni 100 tare da sauya musu wurin zama.
Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yarin Gyara Halinka da ya ziyarci Koton-Karfe, Ja’afu Ahmed ya ce, wasu daga cikin fursunonin sun dawo don kashin kansu, wasu kuma an sake kama su.
Limamin babban Masallacin Koton-Karfe Sa’idu Suleiman Nuhu ya shaida wa manema labarai cewa, an samu ambaliyar ruwan ne sakamakon tunbatsar kogin Osugu, lamarin da ya yi sanadiyar ruhewar gidaje da dama