Shelkwatar hukumar gyaran hali ta kasa reshen jihar Filato ta tabbatar da tserewar wasu fursunoni 4 dake cikin cibiyar gyaran hali dake garin Jos.
Kwanturolan cibiyar Mr Samuel Agunda ne tabbatar da wannan lamarin, ga mane ma labarai a yau juma’a, a garin Jos babban birnin jihar.
Agunda ya ce, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar jiya Alhamis, inda ya dora alhakin hakan, ga rashin Mai da hakali, da jami’an hukumar dake aiki a ranar su ka nuna.
Ya kara da cewa, ” Kunsan mummunan abun da ya faru a cibiyar mu dake Nan garin Jos” inji shi
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Etebo ya koma kungiyar kwallon kafa ta Watford dake Kasar England
“A jiya Alhamis da musalin karfe daya na dare, wasu mutun 4 daga cikin wadanda ake zargi, kuma ake gaf da gurfanar da su a gaban Kotu, da zargin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami, su ka tsere daga cibiyar” a cewar shi.
” Lokacin da na iso inda lamarin ya faru, sai na fahimci cewar, ko dai wadanda ake zargin sun shiga da wani makulli, ko kuma Jami’an dake aiki a ranar basu mai da hankali kan aikin su ba” kamar yadda Aguda ya bayyana.
A karshe ya ce, “Wadanda ake zargin, sun haure katangan cibiyar ne wurin tsere wa, Amma Tuni hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin” inji shi
Comments 1