An samu karin masu dauke da cutar korona 313 a gidajen yarin Morocco bayan da aka yi gwaji.
Hukumomi sun ce gidan yari na Quarzazate da ke tsakiyar kasar ya samu masu 303 cutar ta korona, inda fursuna 10 suka kamu da cutar a gidan yarin Oudaya da ke Marrakesh da kuma gidan yarin Kebir da ke gabashin kasar.
Mafi yawancin mutanen da cutar ta kama fursunoni ne duk da cewa cutar ta shafi wasu ma’aikatan gidan yarin.