Fursunonin Nijeriya tara da ake zargi da balle gidan yari gami da arcewa sun fada komar jami’an ‘yan sandan kasar Ghana a Ada Foah.
Kwamandan caji ofishin din ‘yan sanda ta Ada, Cif Sufuritendan, Francis Somian, ya bayyana cewa sakamakon aikin sintiri na jami’ansu ne ya kaisu ga wannan kamun a ranar Litinin.
Wadanda ake zargin an yi amannar sun balle gidan yari ne daga Nijeriya inda suka shiga Ghana ta kwale-kwale ta hanyar kogin Volta zuwa Ada Foah.
Wadanda aka Kaman suna da niyyar yin nisan tafiya har zuwa Accra a cikin motar bas.
Wadanda aka Kaman sun hada da Emmanuel Obinnah Chiedozie, 27; Steve Eyenuku, 33; Enebeli Lucky, 29; Yommi Usmah, 29; Keli Ekureni, 33; Freedom Yusuf, 25; Obi Onuora, 38; Patrick Chanar, 47; da kuma Bless Eyenuku, 25.
Daga Sulaiman Musa