Akwai fargaba a ranar Alhamis a yayinda wasu Fusatattun Matasa suka ƙone sama da Babura 30 a rukunin gidajen Jakande dake kan hanyar Isheri na Jahar Lagos, bayan zargin wani mai Acaɓa ya hallaka wani mutum.
Jaridar The PUNCH ta gano cewa, ɗan Acaɓan da har yanzu ba’a gano ko waye ba, ya kasance suna bin hanyar da ba tasu ba, a yayinda suka hallaka wannan mutum dake tsaye yana jiran mota.
Ya mutu ne sakamakon wannan banka da Ɗan Acaɓan yayi mashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda sun kama wani Matashi da laifin tura saƙon gargaɗi na zuwan Boko Haram a Ogun
Majiyar mu ta gano cewa, Matasa sunyi fushi da wannan lamari inda suka yi zanga-zanga kan mutuwar wannan mutum.
A lokacin zanga-zangar sun ƙwace wani mashin, kuma suna ƙoƙarin kunna mashi wuta a yayinda wasu ƴan sanda suka ceto shi.
Sun kuma ƙwace Baburan mutane wanda suka bar wurin da lamarin ya faru .
A yayinda masu Baburan suka yi yunƙurin karɓo Mashinan su, sun yi tunanin hallaka su, wanda ya sanya suka bar Baburan suka ruga.
Ƴan Sanda sun kai wani Asibiti da aka jikkata daga cikin masu Acaɓa, a yayinda suka ƙone Baburan da aka bari.
Shugaban Masu Bada Haya na Rukunin Gidajen Jakande Oke Afa, Fatai Oloko yace Ƴan Sanda da Mataimakin Shugaban Cigaban Yankin suna bakin ƙoƙarin su, domin hana masu Baburan ɗaukar Fansa.
Comments 1