A ranar Litinin din nan ne wasu gungun mutane suka kone wasu mutane biyu da ake zargin yan kungiyar asiri ne bisa zargin laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 10, wacce kuma ta mutu, a Ede-Oballa da ke karamar hukumar Nsukka a jihar Enugu.
Wani ganau daga cikin al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa lamarin ya jefa al’ummar cikin bakin ciki.
A cewar majiyar, an tsinci gawar yarinyar ne a wani daji da ke kusa da inda aka cire nono da al’aurarta.
“’Yan asalin garin sun damu da cewa an sami mullar yan kungiyar asiri a cikin yankin. Masu tsafi ne kawai za su yi wa yarinya fyade ta mutu har lahira, sannan su cire mata muhimman sassan jikin ta saboda munanan ayyukansu.
“Don haka ne lokacin da mazauna garin suka ji labarin cewa hukumar kula da unguwanni ta kama wadanda suka aikata wannan aika aika, sai kowa ya garzaya ofishin hukumar.
“Mutane da yawa sun fi karfin jami’an tsaro inda suka kamo matsafan biyu da suka kashe yarinyar suka banka musu wuta suna kallon yadda suka kone kurmus.
“Niyyar jami’an tsaro ne su kai wadanda ake zargin wurin ‘yan sanda amma fusatattun matasan sun fi karfinsu,” inji ganau.
Da aka tuntubi shugaban yankin, da kuma kansilan da ke wakiltar al’ummar, Messrs Val Omeje da Hyginus Ogbu, dukkannin su sun tabbatar da faruwar lamarin.
Sun kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun fito ne daga cikin al’umma.
Sai dai Kokarin da aka yi na tattaunawa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mista Daniel Ndukwe, kan lamarin abun ya ci tura.
A martanin da Ndukwe ya mayar ga gajeriyar sakon da aka aike wa wayarsa ta salula, ya ce, “Na ga sakon ka, zan dawo gare ka.”
A wani labarin kuma na daban.
Ma’aikatan gwamnati 100 sun mutu a Jigawa cikin wata guda
Shirin bayar da gudunmawar fansho na jihar Jigawa da na kananan hukumomi ya ce ma’aikatan gwamnati 100 ne suka mutu a cikin wata guda.
Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Kamilu Aliyu Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da biyan kudaden fansho da na wadanda suka mutuwa a ofishin sa.
Ya ce hukumar ta biya Naira Billiyan 1.215 ga ma’aikata 550 da suka yi ritaya a watan Yulin shekarar 2022.
Kamilu ya bayyana cewa, wadanda suka amfana an kasasu kashi hudu domin biyansu hakkokinsu.
A cewarsa “Kashi na farko ya hada da mutane 411 da suka ci gajiyar aikin bayan sun yi ritaya daga aikin kuma an biya su sama da Naira miliyan 920,331.
“Kashi na biyu na wadanda suka ci gajiyar tallafin su ne iyalan mutane 100 da suka mutu yayin da suke hidimawa jihar, inda suka karbi adadin Naira miliyan 267,329.”
“Kashi na uku na masu cin gajiyar sun kai mutum 8 suna karkashin ma’aunin fansho na mutuwa kuma za su sami Naira miliyan 27, 952 a matsayin hakkinsu.”
“Yayin da kashi na hudu na wadanda suka ci gajiyar tallafin su ne wadanda ba su yi aiki ba har zuwa shekaru biyar, hukumar za ta mayar musu da kashi 8 bisa dari wanda ya kai Naira dubu 201,437 a matsayin hakkinsu.”
Sakataren zartaswar ya kuma jaddada alkawarin hukumar na biyan kowane ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya hakkokinsa a cikin wata daya da ya yi ritaya.
Kazalika ya yabawa Gwamna Muhammad Badaru Abubukar na jihar bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar tare da sakin hakkokin ‘yan fansho a lokacin da ya dace.