Wasu fusatattu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC sun yi kira ga Shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole da ya yi murabus daga kujerarshi.
Fasatattun ‘yan jam’iyyar sun fadi haka ne a Abuja ranar Jumma’a karkashin jagorancin Shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara, Lawal Liman.
Liman ya ce, murabus din Oshiomhole zai samar da yanayin da za a sulhunta rashin jituwar da take jam’iyyar sannan a samu maganin wasu matsalolin da suke addabar jam’iyyar.
Liman, wanda kuma shi ne Kakakin shugabannin jam’iyyar na jihohi, ya ce Oshiomhole ya yi ruf-da-ciki akan komai saboda kama-karya.