Masu tuka babura sama da 100 sun kai hari a Same Global Estate dake unguwar Lokogoma a Abuja domin daukar fansar mutuwar abokan aikinsu biyu.
Lamarin ya faru ne bayan da aka ruwaito wani direban mota ya bugi mahaya Okda a ranar Lahadin da ta gabata kuma ya garzaya cikin gidan domin tsira.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa mahayan Okada sun kona wasu gine-gine guda biyu a yankin.
Mazauna unguwar sun shaida wa wakilinmu cewa, masu tuka babur din sun kai farmaki gidan ne a yunkurinsu na cafke direban mota.
Sun ce dimbin babura ne suka fatattaki direban motar bayan da ya zarce da wasu babura guda biyu.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa jami’an tsaro sun isa gidan ne domin gudun kada a yi asarar dukiyoyi.
Manajan rukunin gidajen m, Mista Adebisi Adelowo, wanda ya zanta da jaridar PUNCH, ya ce, Sama da mahayan babura 100 Hausawa ne sun kai hari a cikin rukuninmu sa’o’i da suka wuce.
Sun yi kokarin kona gidan ta hanyar kona gine-gine biyu a yankin,” inji Shi.
Comments 1