Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya sanya hannu kan dokar da aka yi wa kwaskwarima ta hukunta masu aikata laifin Fyaɗe a jihar musamman ma ga kananan yara.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, hukuncin dai ya haɗar da yin dandaƙa da kuma hukuncin kisa ga duk namijin da aka kama da laifin yin fyaɗe.
A ranar larabar makon jiya ne dai majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da gyaran dokar, sannan aka aikewa gwamnan domin sanya hannu a kai.
Ko a ranar alhamis ɗin da ta gabata manema labarai sun tattaunawa da kwamishiniyar mata ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba, tana mai cewar dama can a shirye gwamnan yake domin sanyawa dokar hannu.
An daɗe ana ɗauki ba daɗi akan dokar daga ƙarshe dai gwamna El-Rufa’i ya amince tare da sanya mata hannu domin ƙaddamar da ita a matsayin doka.