Wata Kotun Majestiri dake garin Ikeja na jihar Legas, a yau Talata, ta bada umarnin tura wani Dan kasuwa mai suna Samuel Asiama mai shekara 42 gidan kaso, bisa zargin yin lalata da wata yarinya yar shekara 9.
Rundunar yan sandan jihar, ta zargi Asiama dake zaune a yankin Isale-Oja na garin Agege a jihar Legas, da yin wa wata yarinya fyade.
Mai shari’ar Kotun A.O Layinka Wacce ta ki amince wa da rokon da Asiama ya yi, Ta kuma bada umarnin da a turashi cibiyar gyaran hali na Kirikiri dake Jihar Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba don mu bata tarbiyya muke harkar Fim ba, inji Rukayya Dawayya
Layinka ta kuma umarci rundunar yan sanda da ta tura kundun laifin wanda ake zargi izuwa ga Daraktan amsan korafe korafen al’uma na jihar . Inda kuma ta dage sauraran karar har izuwa ranar 1 ga watan Disamban shekarar nan da muke ciki.
Tun da fari lokacin sauraran karar, Jami’in dan sanda Mai gabatar da kara Insfecta Lucky Ihiehie, ya bayyana wa Kotun cewa, Asiama ya aikata laifin ne a gidan shi, Kuma a ranar 14 ga watan Agustan da ta gabata, inda ya kira yarinyar zuwa dakin shi, Kuma ya yi lalata da ita.
Kazalika ya bayyana cewa, laifin ya sabawa sashi na 137, na kundun dokar manyan laifuka na jihar Legas, na shekarar 2015.