A jiya ne wata kotu da ke zamanta a Ikeja ta yankewa wani direban motar bas, Tony Akpan, hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bisa samunsa da laifin yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara biyar.
Mai shari’a Abiola Soladoye ya kuma yankewa Ms Itoro Wilson hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin yin rufa-rufa da kuma taimaka wa wanda aka samu da laifin kaucewa shari’a.
Mai shari’a Soladoye ta yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin ne bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi lalata da kananan yara, Wanda ya sabawa sashe na 137 da 415 na dokokin laifuffuka na jihar Legas, na shekarar 2015.
Alkalin kotun, yayin da yake yanke hukunci, ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa Akpan da wanda ake zarginsa, Ms Itoro Wilson..
Alkalin ya kuma bayyana cewar ya amince da shaidan da aka Gabatar a gabansa kan wadanda ake zargi ciki harda binciken likita kan wandanda abun ya shafa.
Sai dai mai shari’a Soladoye ta ba da umarnin a shigar da sunan wanda ake kara na farko a cikin rajistar masu aikata laifin lalata na gwamnatin jihar Legas, inda ya jaddada cewa, ya kamata wanda ake kara na biyu ya fadi gaskiya ba tare da boye gaskiyar lamarin ba.