Hukumar ‘yan sanda a jihar Ogun sun kama wani matashi mai shekaru 23 a duniya Badmus Quadri, da laifin lalata yarinyar makotansu mai shekaru 3 kacal a duniya.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da mahaifiyar yarinyar ta tafi kasuwa domin yin siyayya, kuma ta barta a wajen ‘yan uwanta.
Shi kuwa gogan sai yayi amfani da wannan yarinya ya shiga har dakinsu ya lalata musu ita.
Ko da mahaifiyar ya dawo sai ta lura da jini ya fita daka jikinta nan take ta tambayeta abinda yake faruwa, yarinya da bakinta ta ambaci sunan wanda ya aikata aika-aikar.
Ko da jin haka kuwa, mahaifiyar yarinyar bata tsaya ko ina ba sai ofishin ‘yan sanda na Owode Egbado, nan take ta shigar da kara.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace hukumar tasu bata lokaci ba waken cafko wanda ya aikata wannan laifi ba.
Daga bisani kuma an dauki yarinyar zuwa babban asibitin Idiroko, dake jihar domin duba lafiyarta.