Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta cafke mutane 11 da ake zarginsu da yiwa yarinya ‘yar Shekaru 12 fyade.
Mai magana da yawun hukumar SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar manema labarai a yau Lahadi, da kama wanda ake zargin a garin Dutse.
Jinjir yace wanda ake zargin da ba a bayyana sunayensu ba yace an yi nasarar kama su a garin Dutse.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-an-saki-shugaban-kungiyar-can-reshen-jihar-nassarawa/
Ya kara da cewa wanda ake zargin an kai musu sumame ne yayin da hukumar ta samu bayanan wani daga cikinsu dan shkaru 57 da haihuwa dake kauyen Ma’ai, yayin da aka gansa a kasuwar Limawa dake garin Dutse yana kokarin shawo kan wadda aka aikatawa laifin.
Mai laifin ya bawa hukumar ‘yan sandan karin sunayen mutane 11 da yace sun yi lalata da yarinyar a lokuta daban-daban.
” A yanzu gaba daya an kamo ragowar da ya lissafo kuma zamu mika su zuwa kotu da zarar mun kammala bincike”.