A yau Juma’a ne aka gurfanar da wani matashi mai suna Joseph Osaretin a gaban wata Kotun Majestire dake birnin Benin bisa zargin sace wayoyin alfarma da kuɗin su ya haura naira shida da arba’in.
Ana tuhumar Osaretin ne da laifuka guda biyu da suka hada da haɗin baki don sata da kuma satar kan ta.
Lauayn Mai Shigar da Kara Kehinde Iyawe ya faɗa wa Kotun cewa matashin ya Lallaɓa zuwa gidan wani mai suna Kelvin Oscar dake unguwar Aduwawa Quarters inda ya haura ya caɓe wayoyin da kudin su ya kai naira dubu dari shida da arba’in.
Ya ce laifin ya saɓa wa dokar sashe na 516 da kuma 390 da kuma sashe na tara cikin baka na kundin tsarin mulkin tsohuwar Jihar Bendel na 1976 da a yanzu take Jihar Edo.
To sai dai wanda ake zargin ta bakin Lauyan shi CJ Nkadi ya karyata zargin da ake mishi tare kuma buƙatar vada belinsa.
Kuma Lauyan Yan Sanda dake shigar da karar bai yi jayayya da bukatar bada belin ba.
Nan take kuma Alkalin Kotun Majestiren ya amince da bada belin nasa ian kudi naira dubu dari biyu tare da wani amintaccen mutum guda da zai tsaya mishi.
Yanzu haka an ɗage wannan kara zuwa ranar huɗu ga watan Mayun gobe