An samu fashewar bututun mai da sanyin safiyar Juma’a a Legas.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na safe a unguwar New London dake unguwar Baruwa a Ayobo Ipaja.
Bola Shobowale, shugaban karamar hukumar Ayobo-Ipaja, ya tabbatar da faruwar fashewar.
Babu tabbas ko an samu asarar rayuka ko manyan raunuka. Ana sa ran hukumomin Legas za su bayar da bayanai.
Jami’an bayar da agajin gaggawa da jami’an tsaro sun killace wurin.