Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sha alwashin ba zai ba ‘yan Najeriya kunya ba. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana haka ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama shi da lambar girmamawa ta kasa (GCFR) a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bankuna Yanzu Zasu Iya Bayar Da Katin Ƙasa – FG
Ya ce ya fahimci ma’anar karramawa da aikin da ke gabansa, inda ya yi alkawarin ba zai taba ba wa shugaban kasa da ‘yan Nijeriya kunya ba.
“Ni mutum ne mai saukin kai wanda ke fatan al’ummar Najeriya sun cin gajiyar goyon bayan da suka bani Jama’a sun amince da mu.
Yanzu, wannan babban nauyi zai koma kai kaina. Na fahimci ma’anar girmamawar da aka ba ni a yau da kuma aikin da ke jira.
“Dole ne in gudanar da wannan tseren kuma dole ne in yi aiki mai kyau akan tsaro, tattalin arziki, noma, samar da guraben ayyuka, ilimi, lafiya da samar da wutar lantarki da sauran bangarori. ba zan kunyatar da Jama’a ko kai ba, Mai girma Shugaban kasa.”
A karshe Ya godewa Buhari bisa karramawar da ya yi masa da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya samu kyautar girmamawa girmamawa ta (GCON).
A wani labarin kuma, Sa’o’i Kadan Kafin Rantsar Da Shi, Shugaban Karamar Hukumar Ya Kwanta Dama
Sabon shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, Hon. Lawan Gana, ya rasu ranar Alhamis. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gana ya rasu ne a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Nguru bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.