Watanni biyar bayan sanya dokar shige da fice tsakanin Nigeria da kasashen gamayyar Larabawa UAE, kasar ta tsagaita dokar inda harkokin za su kan kama a biyar ga watan Agusta. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Kasashen Larabawan UAE sun wallafa a shafinsu inda suka ce kasar Nigeria gami da kasashen goma ka iya cigaba da shige da fice a tsakanin kasashen.
Kasashen dai sun hada da India, Pakistan, Sri Lanka, Uganda, Vietnam, South Africa, Afghanistan, Indonesia, Bangladesh da Nepal.
KARANTA:- An kaddamar da bada tallafin Taki ga manoma da ambaliya ya shafa
Kasar tace nan bada jimawa ba zata fidda tsari da dokoki da masu zirga-zirgan ya kamata su sani.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito maku, a watan March ne kasar ta sanar da hana zirga-zirga saboda yaduwar cutar Covid-19.
Haka kuma Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro maku hanyoyi mafiya sauki na zuwa Dubai sune Lagos-Dubai ko Abuja-Dubai.
A wani labarin
An kaddamar da bada tallafin Taki ga manoma da ambaliya ya shafa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kaddamar da tallafin Taki ga manoma dubu uku da iftila’in ambaliya ya shafa a gaba daya jahohin kasar nan.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shine dai Jagoran gidauniyar samar da abinci, wanda mataimakinsa gwamnan Jahar Kebbi Atiku Bagudu, ya wakilce shi a yayin kaddamar da tallafin.
Ambaliyar dai ta zamo sanadiyyar rushe gidaje da gonakin jama’a gami da salwantar abubuwan daban-daban.
Buhari yace an amince da bada tallafin ne don ya rage radadin asarar da manoma suka tafka a lokacin da ambaliyar ta auku.
Shugaba Buhari yace wannan ya zo ne karkashin hukumar samar da tsaron abinci dake karkashin jagorancin nasa.
Yayi kira ga Yan Najeriya da su sanya ido wajan tabbatar da cewa tallafin ya isa ga hannun talakawa da wadanda abun ya shafa.
Kamar yadda yace ya kamata kungiyoyi ma su zaman kansu, da kafafen watsa labarai su taimaka don ganin kowa ya sami tallafin.
Daga cikin kayan da za’a rarraba wajan tallafin sun hada da kayan feshi, masara, irin shuka daban-daban, maganin feshi da sauran kayayyaki noma daban-daban.
Comments 1