Gamayyar wadansu kungiyoyi da ba na gwamnati ba a Kaduna a ranar Litinin a wani tallafin hadin guiwa da suka yi, sun bai wa gidaje 150 kayan abinci a cikin garin Kaduna.
Abincin ya hada da shinkafa, gero, taliyar Indomie, man gyada, magi.
Sun raba kayan abincin ne a g Asha Awuce dake Malali, Kaduna da al’ummar dake filin jirgin kasa na dake Rigasa.
Sun gudanar da wannan tallafin ne a karkashin abin da suka kira; `Humanity Partnership Project’ domin tallafawa marasa galihu a cikin Musulmai da kuma Kiristoci dake Rigasa da Asha Awuce duk a yankin Malami.
Aminu Bashir, shugaban kungiyar ‘Gracious Givers Foundation,’ ya ce kungiyoyi 12 ne suka hadu suka bada wannan tallafi.