Gamayyar Kungiyoyin Magoya Bayan Arewa All progressive conge da kuma Coalition for Civil Society Group sun amince da Sanata Rochas Anayo Okorocha a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa gamayyar kungiyoyin ne suka bayyana hakan a ranar Laraba a taron lakca na kwana daya da aka gudanar a Kano
Kungiyar ta ce Sanata Rochas Anayo Okorocha, mutum ne da Arewa za ta iya aminta da shi. Taron da ya dauki hankulan dubban magoya bayan Sanata Rochas Anayo Okorocha a fadin arewacin kasar ya amince cewa babu wani dan siyasa da yayi daidai da tsohon gwamnan jihar Imo da ya zuba jari a arewa kamar sa.
A jawabin da ya gabatar a wurin taron ‘yan siyasa da suka samu halartan jama’a, ko’odinetan kungiyar na kasa, Alhaji Sadiq Abubakar Yusuf, ya ce babu wani dan siyasa a tarihi da ya sadaukar da kowa don ganin an samu hadin kan kasar nan kamar Sanata Okorocha, domin ya yi abubuwa da yawa da yawancin abokan tafiyarsa ba su yi ba.
‘’Okorocha ya gina makarantu 12, daga ciki shida suna arewa. Ba mu zo nan ne kawai don mu ba shi goyon baya ba, amma don murnar wannan gagarumin kawayen Arewa da suka saka hannun jari a harkar karatunta ba kamar kowa ba,” in ji Yusuf.
Ko’odinetan na kasa ya ce, “Saboda haka, muna da yakinin tantance fitattun ‘yan siyasa da fitattun mutane a fadin Nijeriya cewa Owelle Anayo Rochas Okorocha shi ne mutumin da ya fi dacewa da shugabancin kasar nan a zaben 2023.
Alhaji Yusuf ya bayyana cewa “Sanata Okorocha ya bambamta kansa a cikin shekaru arba’in da suka gabata ta hanyar bayar da gudummawar kason sa don cigaban siyasar Nijeriya, musamman wadanda ake zalunta ta fuskar ilimi, da sana’o’i, da kuma ababen more rayuwa da ma matsuguni.
“Gwamna mai hawa biyu na jihar Imo ya samu nasarori da yawa kuma ya shafi rayuka ta hanyoyi da yawa kusan kowane bangare na mulki kamar yadda ya shafi rayuwa.” ya tambaya wanene a cikin ’yan uwansa ya kara yiwa Najeriya aiki kamar yadda muka gani ga Okorocha.
A wata makala da ya gabatar a wajen taron, Farfesa Aliyu Jibia, ya bayyana Sanata Okorocha a matsayin ginshikin ilimi a Najeriya, inda ya kara da cewa al’ummar makarantunsa na bada shaida kan irin alkawurran da ya dauka na ganin Najeriya ta yi aiki na cigaba.
Farfesa Jibia ya bayyana cewa Cif Okorocha ” yana da taushin hali ga arewa, kuma “muna ganinsa a matsayin daya daga cikin mu fiye da kowa daga sauran sassan kasar nan. ”
Malamin ya cigaba da cewa, domin mu dawo da abun da aka rasa, “Cif Okorocha shi ne amsa a shekarar 2023 saboda ba ya nuna wariya ga ‘yan Najeriya. “