Gamayyar kungiyoyin Arewa 52 sun yi watsi da kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na a saki jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, Mazi Nnamdi Kanu ba tare da wani sharadi ba.
Kungiyar siyasa da zamantakewa ta Pan-Arewa ta kuma zargi Majalisar Dinkin Duniya da nuna son kai a wasu yankuna na kasar nan.
Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman, wanda ya yi wannan zargin yayin wani taron manema labarai a Abuja, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta gaggauta janye bukatar ta na neman Kanu ya samu ‘yanci ba tare da wani sharadi ba daga hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar nan.
Ya kuma shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tashi tsaye wajen kare kasar nan ta hanyar bijirewa da watsi da bukatar.
Suleiman ya bayar da hujjar cewa, tabarbarewar Najeriya ba shakka za ta yi barazana ga zaman lafiya da tsaron daukacin yankin kudu da hamadar Sahara.
Ya ce, “Ba abin yarda ba ne ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya, musamman ma Arewa, Majalisar Dinkin Duniya za ta amince da kafa da sararin da Kanu da IPOB za su yi amfani da su wajen inganta rashin zaman lafiya da kuma fafutukar kawo karshen kisan kiyashi a Nijeriya.