By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ikirarin da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zaben gwamna a shekarar 2019 ba, inda yake cewa wasu manya ne suka dorawa jama’a da karfi da yaji.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa, sabanin ikirari da ya yi a wata hira da ya yi da wata jarida ta kasa, Kwankwaso ya gudanar da wani shiri na magudin zabe, musamman a kananan hukumomin cikin birnin, inda matasa, galibi ba su da katunan masu kada kuri’a don daura damarar aikata wannan aika aika.
Ya ce a fili yake cewa, sa’o’i kadan da fara kada kuri’a aka ce akasarin akwatunan zabe an cika su, sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba ko kuma daukar bayanan masu kada kuri’a ba don haka dole ne ta soke sakamakon daga cibiyoyi da yawa tare da ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda a matsayin kwankwaso na shugaba wanda ake damawa dashi a harkokin gudanar da zabe ya kasa amincewa da sakamakon zaben da hukuma mai zaman kata ta gudanar kuma kotu ta amince dashi.
Kwamishinan yace kwanaki kadan da suka gabata, aka jiyo Kwankwaso a kafafen yada labarai yana gargadin mabiyansa kan dasu kaucewa furta miyagun kalamai amma sai gashi ya kasance mai aikata irin wadannan kalamai da ba su dace ba.
Sannan ya ce bisa ga dukkan alamu, hirar da Kwankwaso ya yi wa kasa kullum inda ya yi yunkurin lalata gwamnatin Ganduje ta yi masa illa fiye da alherin da yake zaton zai samu, wanda kwata-kwata hakan yasa ya yi watsi da ruhin zaman lafiya da sulhu na gaskiya da ya yi wa mabiyansa wa’azi a kwanakin baya don gujewa sabani.
Malam Garba ya bayyana cewa kamata ya yi Kwankwaso ya gode wa Ganduje bisa kammala ayyukan da ya yi watsi da su, inda ya ce al’ummar Kano na biyan kudin sabulu saboda tsarin ci gaba da babu kamarsa da aka kammala a cikin shekaru shida da suka gabata a jihar.
Wadannan ayyuka sun hada da Aminu Dantata Flyover, da titin Yahaya Gusau da titin karkashin kasa na Prince Audu, sai titin kilomita biyar a cikin kananan hukumomin Dawakin Tofa, Ungogo, Warawa, Rano da Tofa, da Titin Mahmoud Salga, da kuma Titin Jaba-Rimin Kebe, kana da aikin samar da wutar lantarki mai zaman kansa a madatsar ruwa Tiga da Challawa da dai sauransu.
Dangane da batun ilimi, wanda Kwankwaso ya yi magana sosai akan sa, kwamishinan ya kara da cewa, a bangaren ilimi gwamnatin Ganduje ta yi ayyuka da dama da suka hada da biyan nauyin sama da biliyan 15 na tallafin karatu ga dalibai marasa galihu a kasashen ketare da gwamnatin Kwankwaso ta tafi ta bari.
Kazalika ya ce ya zuwa yanzu an biya Naira biliyan 3.5 ga dalibai a Sudan; da Naira biliyan 4.5 ga daliban kasar Cyprus, sai Naira miliyan 384 ga wadanda ke karatu a kasar Faransa, yayin da ake ci gaba da biyan daliban dake karatu a kasashen Masar da Indiya.
Malam Garba ya cigaba mai cewa baya ga aiwatar da shirin na ilimi kyauta kuma wajibi na furamare da na sakandare, gwamnatin ta samu damar gudanar da dimbin ayyukan raya ababen more rayuwa a dukkan manyan makarantunta da kuma ba da izinin kwasa-kwasan da suke bayarwa.
Sanarwar ta tabbatar da cewa, duk da yunkurin sulhun da ake yi tsakanin shugabannin jam’iyyar, gwamnatin Ganduje za ta mayar da martani ga duk wani yunkuri na yin watsi da nasarorin da ta samu, kuma ba za ta shagaltu da ci gaba da gudanar da ayyukan da aka zabe ta don su ba.