Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa guda 26 da gwamnatin sa ta aiwatar a fadin jihar nan.
Da yake kaddamar da tashar samar da wutar lantarki ta Tiga wadda ta lashe biliyoyin Naira a karamar hukumar Bebeji a jiya Alhamis, Ganduje ya ce aikin zai bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma ci gaban siyasar jihar.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Gwamnan G5 Ya Rushe Majalisar Zartarwar Sa
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar jiya Alhamis tare da rabawa manema labarai anan Kano.
Gwamna Ganduje ya kuma kaddamar da aikin isar da wutar lantarki da samar da wutar lantarki a matatar ruwa ta Tamburawa dake karamar hukumar Kumbotso.
Sanarwar ta ce aikin zai inganta samar da ruwan sha tare da bunkasa harkar noman rani a jihar.
Manyan ayyuka guda 26 da aka kaddamar sun hadar da wasu tituna Sheikh Mahmud Salga, titin Gashash, titin Bello Kano, titin Kwanar Dala-Makafin Dala, titin garin Bichi, titin Kwanar Akuya, titin garin Karaye, titin Gaya, titin Garin Garo, da sauran su.
A yayin kaddamar da sabon ofishin ‘yan sanda da ke Rijiyar Zaki wanda Shugaban karamar hukumar Ungogo Abdullahi Ramat ya gina tare da samar da kayan aiki da shi, gwamnan ya yabawa shugaban bisa wannan sabon shiri.
A wani labarin kuma: Yan Siyasa Kamata Yayi Su Gina Al’umma Ba Sace Dukiyar su Ba – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ‘yan siyasa su gina jama’a maimakon sace dukiyar al’umma.
Kwankwaso ya yi wannan tsokaci ne a Minna a ranar Alhamis a lokacin da ya zama shugaba a wajen taron kaddamar da zababben gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago.