Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ce ba zai yi wata-wata ba wajen rattaba hannu a aiwatar da hukuncin rataya ga wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Ganduje ya yi alƙawarin sanya hannu a zartar wa matashin da ya aikata laifin Aminu Yahaya Sharif hukunci da zarar lokacin da kotu ta bayar na aiwatar da hukuncin ya yi.
“Kotun ta yi daidai wurin yanke hukuncin. An shaida mana cewa wanda ya aikata laifi na da kwana 30 da zai iya ɗaukaka ƙara, idan bai ɗaukaka ba kuma shi ke nan.
“Bayan sauraron malamai da masu ruwa da tsaki da aka yi a jihar, ba zan ɓata lokacin sa hannu a ka dokar zartar da hukuncin ba da lokacin ya ƙare ko Kotun Koli ta yanke hukunci”, inji gwamnan.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a taronsa da malaman addini da lauyoyi da sauransu masu ruwa da tsaki domin jin matsayinsu game da hukuncin kotun.
Idan ba a manta ba wata kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Aminu Yahaya Sharfi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda yin batanci ga Manzon Allah (SAW) a wata waka da yi.