Gwamnatin jihar Kano ta bada umarni rufe wuraren taro da bukukuwa tare da bai wa ma’aikata umurnin su zauna a gidajensu har zuwa wani lokaci nan gaba. Hakan na zuwa ne a wani mataki da gwamnatin ke dauka na dakile yaduwar cutar korona a jihar.
Har wala yau gwamnatin ta haramta buɗe gidaje ko sinomomin kallon kwallo da ke faɗin jihar, sakamakon karuwar alkaluman masu dauke da korona da ake samu a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba ne ya fitar da wannan sanarwa a yau Talata, inda ya ke cewa gwamna Ganduje ya dau wannan matakin ne bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar jiya Litinin