Gwamman jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce lokaci yayi da yan arewa za su yiwa Bola Ahmed Tinubu kara ta hanyar bashi kuri’unsu, domin zama shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe.
Dr. Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya wajen bikin kaddamar da ofishin kungiyar matasan Arewa, dake goyawa Tinubun baya, inda ya ce babu dan takarar da ya cacanci yan arewa a 2023 irin Bola Tinubu.
A cewar Ganduje al’ummar yarbawa sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gudunmawa a zaben 2015, dan haka lokaci yayi da zasu sakawa yarbawan ta hanyar zaben dan takarar su.
Gwamnan dai ya samu wakilcin shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Danagudi a wajen taron.