Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da bikin rantsar da sabbin kwamishinonin da aka shirya gudanarwa a gobe Laraba domin karrama wadanda suka makale a wani ginin bene mai hawa uku da ya rufta a kasuwar GSM da ke kan titin Beirut a cikin birnin.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan yayin da yake jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su, ya bayar da umarnin daukar tsauraran matakan ceto wadanda suka makale a cikin baraguzan ginin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Enugu Ta Rufe Makarantu Masu Zaman Kansu
Yayin da yake kokawa kan lamarin, ya bayar da tabbacin cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.
Sanarwar ta kuma bayyana bakin ciki ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a ranar Litinin din da ta gabata a sassa da dama na birnin, inda aka yi hasarar kayayyaki na miliyoyin naira.
A wani labarin kuma Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gada, Da Gonaki A Yobe
Ambaliyar ruwan sama da aka shafe kwanaki ana tafkawa ta lalata gadar garin Katarko dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Dr Mohammad Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Talata.