Jam’iyyar APC a Kano ta fada cikin rikici a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ke shirin gudanar da zaɓen shugabaninta a matakin jiha, bisa ga dukkan alamu wata babbar ɓaraka ta kunno kai tsakanin manyan ƴaƴan jam’iyyar a jihar Kano.
Wasu na ganin ɓarakar na da nasaba da zargin da jiga-jigan jam’iyyar suke yi wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere tare da yin gaban kansa wajen yanke hukunci a kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar.
A ranar Talata da daddare ne aka ga wadansu ƙusoshin jam’iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar Dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha’aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam’iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.