A yunkurin shi na bunkasa tattalin arziki, da ganin Matasa sun dogara da kansu, da kuma ganin ya samar da ruwa Mai tsafta a Kano, Gwamnan jihar ta Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci wurin aikin samar da Tashar wutar lantarki na Madatsar ruwa dake garin Challawa a karamar hukumar Karaye na jiha.
Babban Sakataran Gwamnan a kan kafafen yada labarai Abba Anwar ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanar wa da ya fitar a jiya Asabar, Kuma ya aikewa jaridar Dimokuradiyya.
Bayan ya gamsu da yadda ake gudanar da aikin, Gwamnan ya kuma bayyana cewa, wadanda su ke gudanar da aikin sun tabbatar mishi da cewa, zasu kammala aikin nan da watan Yunin shekarar Mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Real Madrid ta shirya siyan Mbappe kan £102
Tashar wutar lantarki za ta samar da karfin 2×3 na ba’aunin Megawat na hasken wutan lantarki ga Masana’antu dake jihar Kano, Futullin Tituna, da kuma amfanu war gidagen al’uma.
Kazalika sanarwar ta ce, ” Mu na da irin wadannan aiyukan guda biyu da muka gada, daya a garin Tiga da kuma na Challawa, Kuma mun zaku muga mun kammala aiyukan a kan lokaci” inji shi.
“Game da batun Tashar wutan lantarki ta Tiga Dam kuwa, mun cimma kashi 95 cikin dari na kammala aikin, Kuma da yaddar Allah za mu kaddamar da shi cikin shekarar nan” a cewar Gwamnan Ganduje.
“Tashoshin wutan lantarki da muke aiilkin su, za mu yi su ne, domin Ma’aikatun jihar Kano, Futullin Tituna, amfanu war kowani Mutum, don haka Muna tabbatar wa da sl”uma cewa, za mu ci gaba da yin aiyuka, domin amfanu war su” a cewar Gamnan.
Da yake bayani a kan tarihin aikin kuwa, Ganduje ya ce, ” Babban kalubale da mu ka fuskanta shi ne, yadda Manoman mu, za su amfana da madatsar ruwan.
A karshe Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce “Amma bisa ga wasu sauye-sauye muncimma dukkannin muradun mu” inji shi.
Comments 1