Gwamnantin jihar Kano tace zata bada fifiko ga ‘yan asalin karamar hukumar Warawa wajen daukan ma’aikan da zasu yi aiki, a sabon asibitin Amina Abdullahi Ganduje dake cikin garin Warawa nan bada jimawa ba.
Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya bayyanan hakan a yammacin Lahadin nan, yayin da yake duba aikin asibitin, inda yace Samar da asibitin zai taimaka wajen inganta lafiyar al’ummar karamar hukumar ta Warawa da kewaye wajen rage musu wahalar daukar marasa lafiyar zuwa manyan asibitocin dake cikin birni.
KU KARANTA: Tinubu Ya Yi Zazzafan Martani Ga Obasanjo, Bayan Ya Zabi Peter Obi
Ya kuma Yi Kira ga mazauna wannan yanki dasu yi amfani da sabon asibitin wajen Kai marasa lafiya gabanin cuta taci karfin su.
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar ta Warawa Yusif Abdullahi Danlasan ya godewa gwamnatin Kano bisa kokarin da take na inganta rayuwar mutanen karamar hukumar,Yana mai fatan ci gaba da samun iriin wannan kulawa daga gwamnatocin gaba.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa gwamnan ya samu rakiyar kwamishinoni da manyan jami’an gwamnantin Kano, yayin ziyarar da suka kai karamar hukumar.
A wani labarin kuma: Ka Cika Alkawarin Da Ka Dauka A 2015 – Iyayen Yan Matan Chibok Ga Buhari
Iyayen ‘yan matan Chibok da aka sace da sauran ‘yan uwa a garin Chibok sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ceto sauran ‘yan matan da ke rike a hannun masu garkuwa da su.
Hakan na kunshe ne a wata budaddiyar wasika ga shugaban kasa mai dauke da sa hannun Yana Galang da Zanna Lawan.