Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi Allah wadai da yunkurin wasu jam’iyyun adawa na marawa matakin sauyin kudin da babban bankin kasar nan CBN ya dauka wanda yace cike yake da rashin sanin ya Kamata.
Ganduje ya bayyana hakan ne a yammacin yau Litinin yayin kaddamar da rabon kayayyakin tallafin da gwamnatin Jihar kano ta Samar ga al’umar kananan hukumomin Jihar nan.
KU KARANTA: Zanga Zamfara karancin kudi ta sanya yan sanda kama mutum 30
Yace kamar yadda aka saba duk lokacin da aka tsinci kai a cikin mawuyacin hali makamancin na annobar Covid_19 gwamnatinsa takan raba kayan abinci don ragewa mutane radadin da suke cikin.
Ya kuma Kara da cewa rabon kayan zai Kai daukacin mazabu Dari hudu da tamanin da hudu dake jihar nan, inda yace duk da cewa gwamnan babban bakin Bai dauki shawarar da aka bashi ba baza su zuba Ido suna kallon al’umma cikin yinwa da fatara ba don haka kowanne mutum zai rabauta da shinkafa Makaroni da kuma man girki.
Da yake jawabi mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya bukaci jama’a su Kara hakuri bisa halin da rashin kudi ya jefa su yana mai cewa tuntuni an San mutanen Kano da juriya da kuma dagewa wajen addu’a duk lokacin da iftila’i irin wannan ya faru.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa mutane da dama ne suka halarci Taron kaddamar da rabon kayan abincin da ya gudana a gidan gwamnatin Kano wanda gwamna Ganduje ya jagoranta.
A wani labarin kuma: Har Abada Ba Zan Koma Real Madrid Da Yin Kwallo Ba — Raphinha
Dan wasan gaban Kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona Raphael Dias Belloli Raphinha ya bayyana cewa, ba zai ta ba bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wasa ba, har karshen rayuwarsa. Kamar yadda Fabrizio Romano ya ruwaito.
Mai shekaru 26 Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyi a kafar yada labarai ta Adri Contreras a yau Litinin.