Gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta kaddamar da shirin fara ciyar da makarantun Firamare 6, 800 a dukkanin fadin jihar.
Da yake jawabi a wurin bikin kaddamar da shirin da ya gudana a Firamaren Jigirya, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce shirin ciyar da daliban Firamaren da suke Aji hudu har zuwa shida an shirya shi domin bunkasa walwalar daliban da kuma karfafa makarantun.
Gwamna Ganduje ya ce shirin yana daga cikin manufofin gwamnatinsa na ba da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da kuma ilimin ‘ya’ya mata tare da hadawa da ilimin Alkur’ani mai girma.
Gwamna Ganduje ya ce; domin dorewar shirin ne bisa kyakkyawan turba ya sanya suka kafa kwamitin da zai rika lura da shirin. Sannan ya ce sun kafa wani kwamiti da zai lura da kayayyakin karatun da kuma tabbatar da bayar da ingantaccen ilimi a makarantun gwamnatin.