Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi da babbar murya ga jama’ar Kano, game da yaɗa barna, yaudara, wuce gona da iri da suka tsiri yi a kwanan nan.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hakan da masu aikata hakan a matsayin masu zagon kasa, kuma hakan tamkar wani yunkuri ne da kafafen sada zumunta suke son koya, ta hanyar yaɗa sautin tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Kabiru Masari wadda ta shafi alakarsa ta siyasa da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
KU KARANTA: Ganduje Ya Biyawa Dalibai Kudin Jarrabawar NECO, NABTEB, NBAIS
Kwamishinan Yada Labarai da kula da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Malam Muhammad Garba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa fitar da sautin na matsayin wani yunkuri na wasu bata gari, wadanda ke da manufar tayar da zaune tsaye.
Ya bayyana cewa daga dukkan alamu wasu mutanen da ba su ji dadin doguwar hirar Tinubu tsakanin Ganduje da Masari ba sun dukufa wajen amfani da lamarin don amfanar da kan su da wata mummunar manufa.
Malam Garba ya kuma kara da cewa tun daga lokacin da gwamna da zababben shugaban kasar suka fahimci wannan mummunar yunkuri na haifar da rashin jituwa a tsakaninsu, kuma ba za su bari wannan kyakkyawar alaka ta aiki da ta yi rauni ba, musamman a wannan mawuyacin lokaci da wasu masu son kai suka lalata komai na kasar nan.
Kwamishinan ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da sauran jama’a da su yi watsi da irin wannan yunkurin kuma su kwantar da hankalinsu da biyayya ga jam’iyyar domin ganin an yi nasarar rantsar da zababben shugaban kasa.
A wani labarin kuma: Duk Gwamnonin Najeriya El-Rufai Ne Ya Ciri Tuta Wajen Fadin Gaskiya Ba Tsaro – Inji Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike
Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna ya ce zai ci gaba da korar ma’aikata, tare da rusa gidaje wadanda aka gina ba bisa ka’ida ba.
Gwamna El-Rufai ya ce zai ci gaba da aikin rushe rushen har zuwa karfe sha daya na daren ranar 29 ga watan Mayu.