Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa shugaban ma’aikatan Gwamnatin Kano, Usman Bala umarnin ci gaba da kula da ayyukan ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Ali Haruna Makoda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano Muhammad Garba ya fitar ya ce shugaban ma’aikatan na Kano zai ci gaba da kula da ayyukan ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano har zuwa lokacin da za a nada wani a mukamin.
A cikin sanarwar gwamna Ganduje ya yi fatan Usman Bala zai yi aiki tukuru don tabbatar da komai ya tafi yadda ya dace a ofishin na shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano.
Yanzu haka dai da dama cikin masu rike da mukamai a gwamnatin Kano, na ta ficewa daga Jam’iyyar APC sakamakon wasu dalilai na kashin kan su.