Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tura takarda ga majalisar dokokin Jahar, inda yake neman majalisar ta amince ya ciwo bashi biliyan 18.7 daga Gwamnatin Tarayya, inda zai yi amfani dasu domin magance matsalolin da cutar Covid-19 ta janyo wa jahar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, Shugaban Majalisar Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta takardar a zauren Majalisar.
A cewar takardar, Gwamnatin Jahar Kano na neman amincewar Majalisar domin bata sukunin samo bashin kuɗaɗe wanda jahohi da dama ƴan majalisun su, sun amince masu su ciwo bashin.

KARANTA WANNAN LABARIN: ASUP tayi fatali da cigaba da gina ‘Polytechnics’ a Najeriya
Yace Gwamnatin Tarayya tuni ta amince ta rarraba sama da Naira biliyan 18 ga dukkanin jahohi 36 a matsayin kuɗin rarar mai na bail out.
Gwamnan ya kuma tura wata takarda ga majalisar dokokin inda yake neman amincewar ta, domin ciwo bashin Naira biliyan 2 dazai siyo motoci ƙirar BRT guda 100 da zasu inganta sufuri.
Takardar tayi nuni dacewar, tuni Gwamnatin Jahar Kano ta bada Naira Miliyan ɗari 500 a matsayin kuɗin ajiya, kuma tana son amso bashi domin ƙarasa biyan kuɗaɗen, wanda hakan zai bada damar kawo motocin, dake da manufar magance wahalhalun sufuri da ake fuskanta a faɗin Jahar.
Bayan an shafe tsawon lokaci ana tattaunawa akan kuɗirin, Majalisar ta amince da ciwon bashin, wanda keda manufar inganta rayuwar ƴan Jahar Kano.
A wani Labarin kuma, Majalisar Dokokin ta karɓi takarda daga ofishin sakataren Gwamnatin Jahar, inda yake tunatar da Majalisar akan rantsar da Shugaba da Mambobin Hukumar Kula da Harkokin Majalisa, gami da sake naɗi, da ɗaga darajar Akawu da Mataimakin Akawun Majalisar ya zuwa shugaban Hukumar kula da Harkokin Majalisa, da Muƙamin Babban Sakatare, da wasu daraktoci a Majalisar Dokokin Jahar Kano.