Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Baffa Babba Dan’agundi a matsayin shugaban riko na Hukumar kula da hakkin mai siye da siyarwa ta jihar Kano.
Wannan ya biyo bayan ajiye aiki da shugaban hukumar Danbazau yayi bisa raɗin kansa, ta hanyar aikewa da gwamnan wasikar dake dauke da bayanin ajiye aikin nasa.
Baffa Babba dai yanzu haka shine shugaban hukumar kula da zirga-zirga Ababan hawa ta jihar Kano, KAROTA.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa a baya dai Baffa shine shugaban riko na Hukumar, wanda daga bisani aka dakatar da shi tare da nada Idris Danbazau.
Wata Sanarwa da Sakataren yada labaran Gwamnan Abba Anwar ya aikowa da Dimokuraɗiyya, ya bayyana cewa nadin nasa zai fara aiki ne nan take.
Daga nan sai gwamnan ya bukace shi kan ci gaba da aiki Tukuru, wanda ta haka ne za a samu nasarar cimma bukatun da aka sanya a gaba.