Gwamnatin jihar Kano ta shirya taron addu’oi ga gwamnonin da aka zaba a kasar nan dama sauran shugabanni da kasa baki daya.
Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci taron addu’ar na makaranta al’qur’ani wanda ya gudana a dakin taro na Afirka House dake gidan gwamnatin Kano a yammacin asabar dinnan, inda yace bisa al’ada sun saba shirya taron yin addu’a a jihar nan don neman dorewar zaman lafiya da karuwarb arziki.
KU KARANTA; Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8
Ya kara da cewa makasudin taron shine don neman taimakon Allah ga zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da kuma gwamnonin da aka zaba a dai dai lokacin da shugaban ke bikin cika shekaru saba’in da daya a duniya.
Gwamnan ya kuma ce an shirya wannan taro ne tsakani da Allah sakamakon matukar bukatar tallafin mahalicci da zababbun shugabannin ke bukata.
Yace yana wannan jawabi ne a lokacin da wa’adin gwamnatin sa ke daf da zuwa karshe a jihar nan.
Taron na yau dai ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da makaranta al’qur’ani
A wani labarin kuma: NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa
Hukumar sadarwa ta kasa NCC na shirin samar da cibiyoyin sadarwa domin bayar da taimakon gaggawa a jihohi 36 na kasar nan, da kuma birnin tarayya Abuja.
Shugaban hukumar Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya bayyana hakan a jihar Enugu ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin taron baje kolin da aka gudanar a jihar, wanda yanzu haka yake ci gaba gudana. Prime Time News ta rawaito.